Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kama Jirgin Ruwan Amurka A Kasar Angola


Maersk Constellation
Maersk Constellation

Hukumomin Angola sun ce masu jirgin ruwan ba su bayyana musu cewa yana dauke da makamai kamar yadda doka ta tanada ba

An kama wani jirgin ruwan Amurka a dab da gabar kasar Angola saboda ayoyin tambayar da ake da su game da irin kayayyakin da yake dauke da su.

Wasu majiyoyi sun fadawa Muryar Amurka cewa jirgin yana dauke da albarusai zuwa kasar Kenya, amma masu jirgin ba su bayyanawa hukumomi cewa su na dauke da irin wannan kaya, kamar yadda doka ta bukata, ba.

Kamfanin da ya mallaki wannan jirgin ruwa mai suna Maersk Constellation, ya bayyana kayan da jirgin ke dauke da shi a zaman mai hatsari. Kamfanin bai bayyana takamammen abinda ke cikin wannan jirgin ruwa ba, amma yace gwamnatin Amurka ta bayarda iznin dauka, kuma ba kasar Angola za a kai ba.

Hukumomin Angola sun ce ma’aikatan jirgin ruwan su 23 zasu ci gaba da zama a tashar jiragen ruwa ta Lobito yayin da jami’ai suke binciken wannan lamarin. Suka ce akasarin ma’aikatan jirgin Amurkawa ne.

Wani kakakin ofishin jakadancin Amurka a Luanda, ya fadawa Muryar Amurka cewa gwamnatin Amurka ta san cewa gwamnatin Angola tana da ikon tabbatar da yin aiki da dokokinta na kwastam.

Jirgin ruwan ya tashi daga Jihar Louisiana, ya yada zango a Dakar a kasar Senegal, ya kuma isa tashar Lobito a Angola ranar litinin.

XS
SM
MD
LG