Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Dan Bindiga Ya Kashe A Kalla Mutane 37 A Thailand, Galibi Kananan Yara


Thailand Shooting
Thailand Shooting

Yau Alhamis, ‘yan sanda a Thailand sun ce wani tsohon dan sanda ya kai hari a wata cibiyar kula da yara a arewa maso gabashin lardin Nongbua Lamphu, in daya kashe akalla mutane 37, ciki har da yara 22, a daya daga cikin munanan hare hare a tarihin kasar da ma duniya baki daya.

Hotuna da bidiyo da aka wallafa a yanar gizo na cibiyar kula da yaran sun nuna wani daki da jini a ko'ina da tabarmi na kwana a warwatse. Hotunan rubutun haruffa da sauran kayan ado kala-kala manne a jikin bangon dakin.

Mahukunta sun ce maharin ya koma gida inda ya kashe matarsa da dansa kafin ya kashe kansa.

‘Yan sanda sun ce ya kuma kashe wasu yara biyu da manya guda tara a wajen cibiyar kula da yaran. Mai dakin nasa da dansa na daga cikin jimlar adadin mutane sama da 30 da suka mutu.

‘Yan sanda sun ce maharin, wanda ke dauke da bindiga da kuma wuka, an bayyana sunan sa da Panya Khamrab mai shekaru 34, tsohon jami’in dan sanda da aka kora daga aiki a bara saboda amfani da miyagun kwayoyi.

Ba kasafai ake samun harbe-harben kan mai uwa da wabi ba a Thailand.

A watan da ya gabata, wani magatakarda a makarantar sojan Thailand da ke birnin Bangkok ya harbe abokin aikinsa, ya kuma kashe wasu mutum biyu sannan ya jikkata wasu kafin aka kama shi.

Harin kan mai uwa da wabi mafi muni na baya-baya a kasar, shi ne na wani soja da ya fusata ya bude wuta a ciki da wajen wani kantin sayar da kayayyaki a birnin Nakhon Ratchasima da ke arewa maso gabashin kasar a shekarar 2020, inda ya kashe mutane 29 ya kuma fafata da jami'an tsaro tsawon sa'oi 16 kafin daga bisani suka kashe shi.

XS
SM
MD
LG