Kungiyar ma'aikatan kotunan shari'a sun fara yajin aikin ne a daidai lokacin cikar wa'adin kwanaki 21 da suka bayar.
Ma'aikatan sun nuna matukar damuwa, da watsi da doka ta 10 da Shugaban kasar Mohammadu Buhari ya rattaba wa hannu a bara, wacce ta ba kananan Hukumomi da bangaren Shari'a damar cin gashin kai.
To sai dai tsohon Dan Majalisar Wakilai wanda da shi ne aka yi gwagwarmayar ganin an bawa wadannan bangarorin gwamnatin damar cin gashin kai, Aminu Shehu Shagari yana ganin Ma'aikatan sun yi gaggawa tare da gajiyan hakuri.
Daya cikin Jami'an kungiyar Gbenga Eludire, ya ce Kashi Na 121 karamin kashi Na 3 na kudin tsarin mulkin kasa ya ce a rika ba bangaren Shari'a kudaden ta kai tsaye.
Gbenga ya ce wannan yajin aikin sun shiga kenan, kuma ba su ba kowa izinin ya sasanta da gwamnonin Jihohin su ba.
Wannan yajin aikin ya kara wa yan Najeriya shiga halin matsi tun bayan fara yajin aikin kungiyar likitoci ta kasa da suka fara kwanaki biyu bayan tafiyar Shugaba Mohammadu Buhari Ingila domin ya duba lafiyar sa.
Saureri Cikkaken Rahoton Medina Dauda a sauti: