Hadakar kungiyoyin masu fataucin kayan abinci da dabbobi ta Najeriya ta fara yajin aikin sai baba ta gani a fadin kasar domin neman gwamnati ta biya bukatun ta na tsaron rayuka da dukiyoyin mambobinta.
Shugaban hadakar kungiyoyin Dakta Muhammad Tahir ya bayyana hakan a wata hira da muryar Amurka a birnin tarayya Abuja.
Tahir ya ce sun rubuta wasiku da dama suna neman gwamnatin kasar ta dauki mataki kan yadda ake kai farmaki da muzgunawa mambobinsu.
Ya kara da cewa rashin sauraro daga hukumomin kasar da kuma matsalolin da mambobin su ke shiga a kullum a yankunan Najeriya daban-daban, ya sa suka yanke shawarar daukar wannan mataki na yajin aiki.
Shi kuwa sakataren hadakar kungiyoyin ta masu fataucin kayan abinci da dabbobi ta Najeriya, Kwamared Ahmed Alaranma Zaria, ya yi kira ga dukan mambobin kungiyar da sauran jama’a baki daya, da su guji karya doka. Ya ce kungiyar ta yi tanadi don kare mambobin ta da sana'ar su.
A nasa bangare, Kabir Salisu Dabai, sakataren kudin kungiyar, ya ce "abin da ke faruwa ba bakon al’amari ba ne, kowa ya sani ba wata sana’a da yanzu za’a kafa ta, ta raya guri sama da irin harkar da su ke yi.
Ya bayyana takaicin cewa "sai a ba mu guri, idan muka gama rayawa shi, sai gwamnati ta fito ta ce gurin ba tsarin kasuwa ba ne, kullum yanayin da muke samun kan mu a ciki kenan a sassan Najeriya daban-daban."
To sai dai ya bayyana cewa a shirye kungiyar ta ke da hau teburin sasantawa domin cimma sulhu da matsaya akan lamarin.
Duk kokarin ji ta bakin ma’aikatar kwadago ta Najeriya don ji daga bangaren gwamnati ya ci tura.
Ga hira da shugabannin hadakar kungiyoyin masu fataucin kayan abinci da dabbobi ta Najeriya.
Karin bayani akan: yajin aiki, Nigeria, da Najeriya.