Wadanda EFCC ta kama tare da tsohon minista Abba Moro su ne da babban daraktan hukumar shige da fice ta Najeriya da wani karamin darakta.
Kamun ya biyo bayan kokarin da ake yi ne domin yi masu shari'a akan badakalar nan ta daukan ma'aikata da ta yi sanadiyar mutuwar mutane sama da goma sha biyar kuma aka yi sama da fadi da nera miliyan dari shida da hamsin.
Hukumar EFCC tace ta gabatar da takardun saka kara a gaban kuliya kuma yanzu rana take jira daga kuliyar domin ta gurfanar dasu.
Kakakin EFCC Baba Mohammad Azare ya yi karin haske inda yace idan jama'a zasu iya tunawa akwai lokacin da aka ce za'a yi karin ma'aikata na hukumar shige da fice ta kasar wato immigration a turance. Cikin tumurtssun da ya faru har wasu sun rasa rayukansu. Banda haka akwai wasu korafe korafe cewa an karbi kudade a hannun mutanen dake neman aiki. Yace tun daga lokacin suke ta yin bincike akan lamarin.
Yanzu dai hukumar ta kammala bincikenta kuma tsohon minista da babban sakatarensa da wani darakta sun shiga hannu kuma su ne da laifi tare da wani kamfani amma basu sami mai kamfanin ba domin baya kasar.
Ga karin bayani