Hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka ta FBI ta yiwa mutanen tambayoyi ne, bayan an fito dasu daga wani gidan yarin hukumar leken asiri Amurka ta CIA dake boye.
Alkali mai shari’a, Colonel James Pohl, ya zartar da hukunci a ranar Juma’a cewa kalaman wadanda ake tsare dasun da suka yiwa FBI, ba za a yi amfani da su a wannan shari’ar da zai kai ga hukuncin kisa ba.
An yiwa wadanda ake tsare dasun tambayoyi ne yayin da ake tsare da su a wata gidan yarin Amurka dake boye a wata kasar da hukumar CIA ke rike da shi. Bayan an mikasu zuwa gidan yarin Amurka dake Guantanamo, wani mai bincike daga hukumar FBI da bai san da batun kalaman da mutanen suka yi a baya ba, shi kuma ya sake yi musu tambayoyi.
Su lauyyoyi masu kare mutanen da ake tsare da su a Guantanamo sun ce tana yiwuwa an canja wani abu a cikin bayanan da suka yi a tambayoyi da jami’an FBI suka musu a baya. A kokarin kare mutanen dake tsare dasun, lauyoyinsu sun ce a binciki yanayin da hukumar CIA ta yi musu tambayoyi.
Mutane biyar da ake tsare dasun sun hada ne da Khalid Sheikh Mohammed, wanda ake tuhuma da shirya harin na ranar 11 ga Satumban 2001.
Facebook Forum