Jami'an Amurka da suke yaki da ta’addanci sun ce duk da irin nasarori da aka samu a yaki da ta'adanci da sake kwato yankunan daka hannun kungiyoyin ta'adda kamar ISIS da Al Qa’ida, yanayi da harkokin ta'adanci sun kara sarkakiya.
Kungiyoyin ISIS da Al-qaida da kawayen su, sun nuna suna kan bakarsu, da nuna juyriya, da badda sawu” a cewar wani babban jam’in yaki da ta’addanci Nathan Sales a jiya laraba, ya kuma kara da cewa kungiyoyin sun sun sauya take takensu saboda kara matsa kaimi wajen yaki da ta’addanci a Iraqi da Somalia da sauran wuraren da abin ya shafa.
Sales yayi bayanin ne a wani jawabi da yayi wa manema labarai kan bayanan ma’aikatar harkokin wajen Amurka na shekarar 2017 akan ta’addanci wanda ya nuna cewa kungiyin ISIS da Alqaida sun kara bazuwa, kuma sun koma amfani da yanar gizo wajen ingiza magoya bayansu a wurare daban daban su kai hare-haren ta'addanci.
Facebook Forum