Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyoyin Ma’aikata Da Masana Sun Fara Tsokaci Kan Miliyoyin Kudin Da Shugaba Buhari Ya Umurci A Ba Jihohi


Biyo bayan amincewa da umarnin da shugaban kasa Muhammadu Buhari, yayi na a rabawa gwamnonin jihohi 36 tare da babban Birnin Tarayya Abuja, miliyoyin daloli da kungiyar bada rancen kudi ta kasa da kasa watau Pariss Club, ta dawowa Nijeriya da su.

Yanzu haka kungiyoyin ma’aikata da masana sun fara maida martani na yadda yakamata ayi, domin kawo yanzu akwai wasu sama da Naira biliyan uku da ake zargin wasu gwamnoni da rashin bin ka'ida da tsare-tsaren da aka basu na yadda za su yi amfani da kason farko.

Ana zargin cewa gwamnonin sun yi abun da suka ga dama da kudaden ko da yake gwamnati ba ta bayyana sunayen jihohin da suka yi gaban kansu da kudin ba.

A farkon makon nan ne Shugaban kasa Muhammad Buhari, ya ba ministar kudi da gwamnan babban bankin kasar umurnin sakarwa jihohi Naira Biliyan 500, cikin gaggawa. Kudaden na cikin rarar da aka samo daga kungiyar Paris Club, da ta mayarwa Najeriya saboda ta biya fiye da bashin da kungiyar ke binta.

Sai dai yayin da ake shirin raba masu kudaden, akwai wasu sama da Naira Biliyan uku da ake zargin wasu gwamnoni da rashin bin ka'ida da tsare-tsaren da aka ba su na yadda za su yi amfani da kason farko. Domin ana zargin cewa gwamnonin sun yi abinda suka ga dama da kudaden ko da yake gwamnati ba ta bayyana sunayen jihohin da suka yi gaban kansu da kudin ba.

To sai dai kuma yayin da ake fatan za'a bi ka'ida a wannan karon, tuni kungiyoyin ma’aikata da masu fashin baki suka soma tsokaci. Comrade Muhammad Baba Shelleng, dake zama jami’in hulda da jama’a na kungiyar ma’aikatan kananan hukumomin Najeriya, NULGE, reshen jihar Adamawa, yace su kam sun zura ido suga ko wannan karon za’a tuna dasu ganin cewa a baya an mance dasu.

Kamar yadda bayanai suka nunar, duk da dauki na bail-out,baya ga kason farko na kungiyar Paris Club, ta bada, har yanzu ma’aikata a wasu jihohin kasar na cikin mawuyacin hali na rashin samun albashi, batun da Mallam Yakubu Musa Uba, dake zama daya daga cikin shugabanin kungiyar wakilan kafofin yada labarai a Najeriya ke ganin akwai abun dubawa.

Domin Karin bayani, ga cikakken rahoton Ibrahim Abdul’Aziz.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:37 0:00

Facebook Forum

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG