Ma’ajiyun suna dauke ne da sunayen ‘yan uwa ko yaran masu zarmiyar da kuma lambobin shedar ajiyar banki mai dauke da tambarin yatsun hannu, wanda za a iya amfani da su wajan gano asalin mai ajiyar.
Alhaji Garba Umar Yobe, tsohon babban jami’in banki ne, kuma ya bayyana cewa wannan matakin yana bisa doka, ya kuma kara da cewa yawancin asusun ajiyar ana fara sa masu kananan kudade ne, sai daga baya a fara aje miliyoyi, dan haka doka ta tanaji a bada rahotanni duk sati akan irin su.
Tun lokacin da aka kaddamar da shirin fallasa masu zarmiya ake samun makudan kudade, Su kuma masu tsegumin suna samun ladan matakin da suka dauka, kuma ‘yan siyasa da shugabannin al’umma na yabawa wanna a mataki da aka dauka.
Shugaban jam’iyyar APC mai mulki Alhaji Inuwa Yahaya, ya bayyana farincikinsa akan wannan mataki da aka dauka akan wadanda ya kwatanta da kaska, mai makalewa jikin dabba tana shan jininta, wato barayin dukiyar Najeriya.
Mai taimakawa shugaban kasa kan labaru Shehu Garba, ya ce ma’aikatan banki sun taka rawa wajan fallasa irin wadannan kudade, sai dai wasu kan bukaci a raba biyu a basu kashi guda wanda hakan bai dace ba domin dukiyar kasa ce, amma dokar ta bada hurumin a ba duk wanda ya kawo irin wadannan bayanai wani kaso daga ciki.
Ga cikakken rahoton Nasiru Adamu El-hikaya daga Auja.
Facebook Forum