Manufofin sun hada da yadda baki zasu shiga Najeriya, da kuma yadda zasu zauna a kasar, ministan cikin gida Laftanar Janar Dambazau, mai ritaya ne ya kaddamar da manufofin.
Da yake jawabi wurin kaddamar da manufofin, ministan ya bayyana cewa kalubalen da ake fuskanta a kasar sun hada da yadda ake shigar da makamai da sace yara kanana, maza da ‘yan mata, dan haka za a mayar da hankali kan lamarin. Sai kuma baki wadanda suka shiga kasar, dokar ta bada damar a san daga inda suke, kuma ina zasu je da kuma dalilin da ya kawosu.
A wannan sabuwar manufa, masu neman takardar izinin zama Najeriya zasu sami takardar cikin sauki, domin an sauya tsofafin hanyoyin da ake bi wajan samun takardar kamar yadda shugaban hukumar shigi da fice Muhammadu Baban Dede ya bayyana.
Shugaban ya bayyana cewa dokar ta bada dama akan hukunta duk wanda aka kama da laifin safarar mutane, za a kama shi a kaishi gaban alkali a kuma a sa masa tarar Naira Miliyan daya kuma a kulle shi har na tsawon shekaru goma. Kuma dokar ta bayyana cewa duk bakon da zai zauna har ya zarce kwanaki Tamanin, to wajibi ne yayi rajista a jiha ko karamar hukumar da yake zama.
Wadannan manufofi sun maye gurbin wadanda aka kwashe shekaru Hamsin da uku ana amfani da su.
Ga rahoton Madina Dauda daga Abuja.
Facebook Forum