Tsohon shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa Sanata Ali Ndume, ya bayyana cewa yana da niyyar shigar da karar shugaban hukumar kwastan dinne a sakamakon wata sabuwar doka da shugaban ya bullo da ita wadda ta bukaci biyan kudin futo kan dukkan motocin da ke cikin kasar komai tsufansu.
Sanata Ndume, ya bayyana cewa wannan doka da shugaban hukumar kwastan ya bullo da ita ta sabawa alkawarin da suka yiwa al’ummar Najeriya, ta dalilin haka ne Ndume, ya ce yayi niyyar kai shugaban kotu a madadin jama’ar kasa.
Ya kuma kara da cewa ‘yan majalisar dattawan sun kauce, domin a maimakon su yi abin da ya dami jama’a, sai suka raja’a kan maganar sa kayan sarki, kuma daya daga cikin abinda bai amince da shi ba, shine yadda wasu suka mayar da majalisar tamkar fadar wani da wani.
Da dama daga cikin dattawan suna ganin yadda aka mayar da majalisar tamkar fadar Saraki da Dino, kuma ya kamata su dauki mataki akan wasu abubuwa da ke gudna a majalisar amma sun yi kunnen uwar shegu wai da sunan a zauna lafiya.
Shi kuwa Sanata Kabiru Marafan Gusau, ya ce yana matukar goyon bayan da majalisa ta dauka akan shugaban hukumar kwastam din, domin idan an duba da kyau, majalisar dattawa aikinta ne.
Ga cikakken rahoton Madina Dauda, daga Abuja.
Facebook Forum