A cikin wasikar da suka mika sun zayyana batutuwa da dama da suke da nasaba da yadda suka ga shugaban yana mulkin kasar har da mukaman da shugaban bai riga ya nada ba.
Abdulhamid Abdullahi Dantarko shugaban zanga-zangar yace akwai mutane da basu da gaskiya dake cikin gwamnatin Buhari. Yace kungiyarsu ita ce take tsakanin shugaban kasa da talakawan da suka zabeshi. Da karfin talakawa da taimakonsu aka zabeshi.
Abdullhamid Dantarko yace suna son shugaban kasa ya gane cewa akwai mutane da basu da adalci, mutane masu son cin hanci da yin almundahana da son rashawa duk suna cikin wannan gwamnatinsa. Kungiyar ta bukaci ya ciresu ba domin komi ba saboda suna son adalci a kasa.
Ita ma shugabar mata ta kungiyar Hajara Yusuf ta yi gargadi ne ga wadanda kungiyar ke ganin suna yiwa gwamnatin Buhari zagon kasa. Tace ko su fice daga gwamnatin ko kuma shugaban ya fitar dasu.
Shi ma shugaban habaka matasan arewa Imrana Wada Nas ya yi tsokaci akan mukaman da ba'a nada ba. Yace duk matsalar da aka samu tsakanin shugaban kasa da jam'iyyarsa su suka haddasata. Yace mutanen da shugaba Buhari ya kwaso basu iya gaya mashi gaskiya. Suna shakkar fada mashi gaskiya. Basu ma da cancantar su yi aiki dashi. Yace kamata ya yi a laluba a nemo mutanen da suka cancanta a basu aiki. Duk abun da suka yi shi shugaban kasa za'a kalla saboda shi ya nadasu.
Nas yace Allah ya taimaki shugaban kasa ya nemo mutanen kirki su yi aiki dashi. Duk wanda aka fahimci ba zai iya ba shugaba ya yi mashi godiya ya sallameshi kana ya dauko mutumin kirki ya sa.
Ga karin bayani.