Idan ba'a dauki matakan gaggawa na murkushe sace mutane da fashi da makami da yanzu suka addabi mutane ba to ko ta'adancin 'yan Boko Haram da yaki dasu zai zama tamkar wasa ne.
Kwararrau akan alamuran dokoki da sadarwa ta zamani sun bayyana abubuwan da ya kamata mahukunta su yi. Farfasa Almustapha Usuju kwararre akan sha'anin dokoki da Malam Saleh Haliru akan alamuran sadarwa na zamani sun nuna cewa dole ne a yi anfani da ilimi da naurori na zamani domin yakar matsalar.
Farfasa Usuju yace mutane da dama sun koma satar jama'a domin ta fi basu kudi fiye da yin fashi saboda za'a kawo masu kudi lakadan a sauke masu. Amma abun da yake bashi mamaki shi ne da waya masu fashi ke magana kuma duk da naurar dake iya nuna inda mutum yake magana har yanzu 'yansanda basa iya gano inda miyagun mutanen suke.Ba'a samu a kamasu ba.
Yace lokacin da Boko Haram ta shigo da kwanta kwanta aka fara kafin su koma arewa masu yamma su kuma 'yan Boko Haram suka mamaye arewa maso gabas.
Malam Saleh shi ma yace akwai sakaci daga bangaren jami'an tsaro. Idan da kasar zata kashe makudan kudi ta sayo jiragen sama masu saukar angulu dake dauke da wasu kamarori na musamman dake daukar dumin jikin mutum dake gano koina mutum yake za'a ganosu a shawo kan matsalar.
Ga karin bayani.