Gwamnan Zamfara Abdulaziz Yari Abubakar shugaban taron wanda kuma shi ne shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya ya yiwa manema labarai bayanin abubuwan da suka cimma a taronsu.
Yayinda yake magana da 'yan jarida yace zasu sa ayyukan noma gaba da sarafa kayan gona da aka noma. Zasu maida karfi kan sha'anin ilimi da inganta wutar lartanki saboda idan babu ita cigaba zai yi wuya.
Jihohin zasu dubi sha'anin ma'adanan kasa da Allah ya albarkacesu dasu. Zasu samar ma dimbin samarinsu da yanzu basu da aiki aikin yi.
Saidai wasu 'yan Najeriya na ganin tarukan gwamnanonin tamkar fafar gora ce a ranar tafiya lamarin da gwamna Abdulaziz Yari Abubakar ya musanta. Yace ba sabon abu ba ne cewa sun shigo domin inganta rayuwar al'umma. Babu yadda za'a inganta rayuwar jama'a babu aikin yi, babu abinci, da. tsaro.
Gabanin taron Kanon ko a makon jiya gwamnonin sun yi makamancinsa a jihar Katsina bayan tarukan da suka dinga gudanarwa a biranen Kaduna da Abuja kan batutuwa daban daban.
Bayan sun kammala taron gwamnonin bakwai sun gana da wakilan 'yan kasuwar Sabongarin Kano da ta kone a makon jiya. Tun farko batun konewar kasuwannin Kano da na Birnin Kebbi na daga cikin abubuwan da suka tattauna a taronsu. Shugaban gwamnonin Abdulaziz Yari Abubakar ya yi masu alkawarin taimaka masu.
Ga karin bayani