Matsalolin dake kawo nakaso wajen samar da aiyukan lafiya a Najeriya, sun hada da rashin kayan aiki da kwararrun likitoci a asibitoci, da kuma rashin albashi mai inganci.
Likitan dake jagorantar wani shirin kakakin majalisar tarayya Barrister Yakubu Dogara, na tallafawa jama’a, a kiwon lafiya a jihar Bauchi, Dr. Haruna Kibu, shine ya yi wanna furushin a garin Bauchi.
Ahmed Yarima, Sarkin Malaman Misau, wanda ya wakilcin kakakin majalisar yace yayi ne domin ya agazawa jama’ar, jihar Bauchi, taimako ne da yake yin a kiwon lafiya, babu wasu kudade da ake baiwa ‘yan majalisa na masamman domin taimakon jama’a,.
Tallafawa ta fanin kiwon lafiya , samar da ruwa da gyara makarantu da wakilai keyi suna yi ne a matsayin tallafi babu wani kasafi na masamman da aka yi daga cikin albashi ko alawus, da ake bada wan a saman gari cewa ‘yan majalisu suyi wannan.
Amma in ji cewar mai taimakawa Gwamna jihar Bauchi a fanin labarai da hulda da jama’a, Sabo Muhammad,yace akwai hakki kan wakilan jama’a suin bada tasu gudumawar.