Wannan bayanin na kunshe a wata takarda da shugabanta Mr, Manassah Nayangon, ya gabatarwa taron manema labarai da ta kira a Yola fadar jihar Adamawa, Kungiyar ta ce akwai kwararan bayanai da ta dogara da su, tana nuni da harin baya-bayan nan da aka kai kauyen Balawo inda aka kona shi kurmus makon da ya gabata.
Mukaddashin kwamishinan ‘yan sanda na jihar Adamawa Alhaji Modu, wanda da ya tabbatar da harin, ya ce ana ci gaba da bincike ko da yake kawo yanzu babu wanda aka kama.
Wasu daga cikin shugabannin kungiyar Mr Caleb Tabwas da Samuel Buba, da wakilin Muryar Amurka Sunusi Adamu, ya zanta da su jim kadan bayan taron manema labaran sun shaida masa dalilin da yasa suka kira taron. Sun ce suna juyayin rashin daukar mataki kan takardar koke da suka gabatarwa gwamnati inda suke tuhumar wasu da ke da hanu a harin ranar ashirin da hudu ga watan Junairun wannan shekara da ya yi sanadiyyar asarar rayukan mutane sama da sittin.