Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Marubutan Arewa Ta Bukaci Gwamnati Ta Ɗauki Matakin Gaggawa Kan Matsalar Tsaro


KUNGIYAR MARUBUTA AREWA A YANAR GIZO
KUNGIYAR MARUBUTA AREWA A YANAR GIZO

Ƙungiyar marubutan Arewa "Arewa Media Writers" ta turawa shugabannin hukumomin tsaron Najeriya sakonnin halin da al'ummar Arewa suke ciki na taɓarɓarewar tsaro, musamman a ƴan kwanakin nan.

Haka zalika ƙungiyar ta buƙaci gwamnatin ƙasar da ta tashi tsaye kan taɓarɓarewar tsaron da yayi muni a yankin Arewa dama ƙasar Najeriya baki ɗaya.

Ƙungiyar ta bayyana hakan ne, a cikin takaddun ƙorafi da ta turawa hukumomin tsaron mai ɗauke da sa hannun shugaban ƙungiyar na ƙasa Comr Abba Sani Pantami, inda ƙungiyar ta bayana irin takaici da jimamin halin da al'ummar Arewa suke ciki, na rashin zaman lafiya, rashin kwanciyar hankali, ga kuma talauci da tsadar Rayuwa da al'ummar yankin suke ciki.

Kungiyar ta kuma kara da cewa za ta ci gaba da ƙoƙarin da ta ke yi wajen kawar da duk wasu labaran ƙarya da ka iya kawo matsala a wurin yaƙi da ƴan ta'addan tare da cigaba da wayarwa al'umma kai domin samun ci gaba da haɗin kai da cikakken haɗin kan Al'ummar mu.

A wani bangaren kuma shararriyar yar gwagwarmaya a Najeriya Aisha Yesufu ta bude wani shafi a yanar gizo inda ta bukaci yan kasar su mara mata baya a korafe korafen matsalar rashin tsaro da yankin arewa ke fuskata, a wani mataki na janyo hankalin gwamnati da masu ruwa da tsaki kan sha’anin na tsaro.

A cewar ta ya kamata hukumomin tsaro su kara kaimi wajen binciko masu hannu a cikin aikata miyagun laifuffuka a Najeriya tare da hukuntasu. Kazalika a samu hadin kai tsakanin al’umma da jami’an tsaro.

XS
SM
MD
LG