Taron ya samu jagorancin tsoffin shugabannin Najeriya, Olusegun Obasanjo da Janar Abdulsalami Abubakar inda taron ya yi kira da babbar murya ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya tanadi kafa ta musamman da zai rika amsar shawarwari da ra'ayoyin ‘yan Najeriya wadda zai sa gwamnati ta zamanto mai kima da fahimtar halin da al'umma ke ciki.
Jawabin bayan taron, wanda Ambasada Ahmed Magaji ya karantawa manema labarai, a ciki har da Wakiliyar Muryar Amurka Medina Dauda.
Ambasada Ahmed Magaji ne ya karantawa manema labarai jawabin bayan taron kwamitin wanda baya ga tsoffin shugabannin, ya kunshi shugabanin addinai Sultan Sa'ad Abubakar na III da Kadinal John Onayekan da manyan tsofin masu Shari'a da tsofin Sakatarorin Gwamnati da Tsofin masu ba shugaban kasa shawara a harkar tsaro da Kungiyar Kwadago.
Kazalika kwamtin ya kunshi Kungiyar Malaman Jami'o'i, da Kungiyoyin Arewa, Afenifere na Yarbawa, Ohaneze N'digbo da gamayyar kungiyoyi mata da na matasa kamar yadda
Ambasada Magaji ya ce wannan taro ya yi la'akari da halin da kasa ta ke ciki dab da lokacin da ake tunkarar zabe na shekara 2023 a cikin halin mumunan rashin tsaro da kasar ba ta taba gani ba.
Saboda haka, ake ba shugaba Muhammadu Buhari shawarar ya gaggauta sa hannu a dokar zabe ta shekara 2021 da Majalisar dokoki suka aike masa, saboda a tsaftace harkokin zabe a kasar baki daya.
Magaji ya kara da cewa, ita kanta Majalisar Dokoki ta gaggauta kammala garambawul da ta ke yi a kundin tsarin mulkin kasar saboda su tafi tare da sabuwar dokar zaben domin a samu a yi zaben shekara 2023 cikin kwanciyar hankali da lumana.
Magaji ya ce suna kira ga dukkanin Shugabanin Kasa, Sarakuna da dattawa da kwararru da masu ruwa da tsaki da su taka muhimmiyar rawa wajen hadin kan kasar.
Ya kara da cewa wannan kwamiti ne na dindindin wanda kowa ke iya tuntubar shi da shawarwari a ko yaushe.
Da ya ke amsa tambayar wakiliyar Muryar Amurka bayan jawabin taron Mai magana da yawun Kungiyar Dattawan Arewa Dokta Hakeem Baba Ahmed ya yi karin haske akan matakin da kwamitin zai dauka in da ya ce za su aikawa Majalisar Dokoki da na Jihohi da Shugaba Mohammadu Buhari da kuma Gwamnoni Kasar sakamakon taron domin su dauki mataki akai.
Kwamitin ya kwashi kwanaki biyu yana tattaunawa ta hanyoyi daban daban domin samun mafita ga halin ha'ula'i da kasar ta samu kanta a ciki.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: