Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya yi kira ga dakarun Najeriya da su kara kaimi a yakin da suke yi da ‘yan ta’adda ta hanyar kai wa ga maboyarsu da ke cikin dazuka.
A cewar Zulum, wannan ita ce mafita muddin idan ana so a magance matsalar hare-hare ‘yan ta’addan Boko Haram a yankin jihohin arewa maso gabashin Najeriyar.
“Ina kira ga sojojin Najeriya da su kutsa kai zuwa inda ‘yan ta’addan da suka ki mika wuya ke buya. Ya zama dole mu bi su har mafakarsu.” Gwamnan ya ce.
Kalaman na Farfsesa Zulum na zuwa ne yayin taron kungiyar gwamnonin jihohin yankin arewa maso gabashin Najeriya shida wanda ya wakana a jihar Yobe cikin sirri kamar yadda gwamnatin jihar Borno ta fitar cikin wata sanarwa.
“Ya zama wajibi mu kakkabe burbushin ‘yan ta’addan ta hanyar bin su har maboyarsu.” Zulum wanda shi ne shugaban kungiyar ya ce.
Ya kara da cewa, al’amuran da ke faruwa a ‘yan kwanakin nan a yankin na arewa maso gabashin Najeriyar, na nuni da cewa akwai alamun yakin da ake yi da mayakan na Boko Haram ya kusa kawo wa karshe.
Yayin jawabinsa na maraba, gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni, ya yi magana kan manufofin kungiyar gwamnonin da yanayin tsaro a yankin da kuma irin nasarar da sojojin Najeriya ke samu.
Baya ga gwamna Zulum da Mai Mala Buni, gwamnan jihar Gombe Inuwa Yahaya ya samu halartar taron yayin da gwamnonin Adamawa, Bauchi da Taraba suka tura mataimakansu.
Taron kungiyar gwamnonin arewa maso gabashin Najeriyar wanda aka yi a karo na shida na zuwa ne yayin da matsalar tsaro a arewa maso yammacin kasar ke kara tabarbarewa, inda ‘yan fashin daji ke kai hare-hare da satar mutane domin neman kudin fansa.