Baya ga Ministan lafiya da kungiyar tace zata yi ‘kara gaban kotu, har ma da babban sufeton ‘yan sanda na kasar da kuma kwamishinonin ‘yan sanda na jahohi da kuma na birnin tarayya Abuja, sai kuma kwamishinonin lafiya na jahohin Najeriya 36.
A wani taron manema labarai da shugaban kungiyar na ‘kasa Barista Abdullahi Bulama Bukarti, yace neman takardar bayar da izini da kuma bayar da ita haramtattun ayyuka ne a Najeriya.
Yawancin lokuta wasu asibitoci na kudi da na gwamnati suna dagewa suke ba zasu taba maras lafiya ba har sai sun kawo takarda daga ‘yan sanda kafin su taba marasa lafiya. Haka kuma karbar takardar na daukar lokaci, da kuma tambayar kudade ga wadanda suka je nema.
Hakan yasa kungiyar lauyoyin tayi nazari har ta gano cewa babu wata doka da ta tanadi hakan. Akwai dokar Najeriya ta National Healthcare Act, da ta tanadi cewa haramun ne likita ko ma’aikacin jiya ya ‘ki yiwa wani aiki kan kowanne dalili.
Ko a watan jiya ma rashin samar da takarda daga ‘yan sanda ga likitoci yayi sanadiyar rasuwar wani Mallam Ibrahim Badamasi na kauyen Gundutse a yankin karamar hukumar Kura a jahar Kano, bayan da ya shafe kimanin sa’o’i 36 da albarushi a jikinsa a Asibitin Nasarawa.
Kungiyar dai ta bayar da wa’adin wata guda domin hukumomin da lamarin ya shafa su dauki mataki, ko kungiyar ta garzaya kotu.
Domin karin bayani saurari rahotan Mahmud Ibrahim Kwari.