Tun farko dai shugaba Jammeh ya amince da shan kaye a zaben har ma ya taya dan adawan murna amma daga baya ya canza ransa tare da zargin cewa ya gano an yi magudi a zaben.
Manjo Janar Yakubu Usman mai ritaya masanin tsaro a yankin Afirka ta yamma yace suna fargaban sabon matsayin na Yahya Jammeh ka iya haddasa tashin hankali a kasar da take karama. Yace da zara an soma tashin hankali kasar gaba daya zata rude.
Shi ma Dr. Bawa Abdullahi Wase yace fargabar itace tashin tashina da fitina. Yace shugabannin dake son rike iko a hannunsu ta ko halin yaya ba tare da tausayawa kowa ba suke kawo mugun tashin hankalin jama'a. Dalili ke nan a cewarsa da ake samun yaki tsakanin wannan kabila da waccan a kasa daya.Irin wannan halin da Jammeh yake son ya nuna babu abun da zai kawo illa tashin hankali da tarnaki. Saboda haka ya kamata a yi kokari a shawo kansa.
Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.