Lokacin da suka isa asibitin da likitan ya duba takardar da suka mika mashi sai yace su biya nera dubu hamsin amma kuma basu da kudin nan take saboda basu tafi da kudi ba.
Sun roki likitocin su yi mata aikin kana daga baya sai su nemi yadda zasu biya kudin amma duk wani lalama da suka yiwa likitocin sai suka ki kememe su yi mata aiki. Likitocin sun ce su ba laifinsu ba ne. Ba zasu yi aikin ba sai an bada nera dubu hamsin nan take.
Malama Ramatu Salisu uwar Habiba Sa'adu wadda ke da juna biyu amma ta rasu sanadiyar rashin yi mata aiki ita ce ta bayyanawa Muryar Amurka irin halin da suka samu kansu ciki inda nera dubu hamsi tafi ran diyarta.
Sakacin likitocin dake asibitin kwararru a Nasarawan Kano ya sa Habiba ta rasa ranta.
Malam Sa'adu Aliyu mijin Habiba marigayiya yace sun kai kusa awa daya suna neman inda zasu kaita cikin asibitin. Daga bisani dai aka kaisu sama, da likitan ya ga takardar yace aiki za'a yi mata amma sai an biya nera dubu hamsin.
Da karshe dai sun dauki matar sun shiga da ita inda suka ja labule. Shi ke nan basu ji komi ba sai dai labarin ta rasu. Mijin matar yace abun da yake so shi ne a bashi hakkinsa.
Yanzu dai kungiyar kishin kare hakkin 'yan Najeriya da Barrister Abdullahi Bulama ke jagoranta tace zata dauki matakin shari'a game da batun saboda acewarsa abin da ya faru sakaci ne.Kungiyar zata nemi hukumar dake kula da ayyukan likitoci ta hukumta wadanda suka yi danyan aikin. Kana zasu je kotun Kano su nemi diya.
Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari da karin bayani.