Kungiyar kwadago a Najeriya tace babu ja da baya akan yunkurin tafiya yajin aiki na jan kunne daga 12 na dare laraban nan akan batun samun karin albashi na naira 65,500.Shugaban kungiyar a Najeriya Kwamared Ayuba Wabba yace tun lokacin da suka baiwa Gwamnatin Nigeria wa'adi a Makonni 2 da suka gabata akan bukatar biyan sabon tsarin albashi na Niara dubu 65 da Naira 500 to har ya zuwa yammacin Talatan nan, babu wani bayani daga Bangaren Gwamnatin Nigeriar.
Yayi magana da Muryar Amurka a wani taron kasa na kungiyar malaman Najeriya da akayi a Minna. Shugaban kungiyar kwadago a jihar kaduna Kwamared Adamu ango yace ya zuwa yanzu sun kusa sasantawa da jihar Kaduna domin an mayar da malamai dubu 13 a bakin aiki.
Domin karin bayani, Saurari rahoton Muystapha Batsari..
Facebook Forum