Mutane 12 suka mutu a garin Gidan Iddar dake cikin jihar Touha a kasar Niger sanadiyar shaye-shayen kwayoyi iri iri da suka hada da wata kwaya mai suna madara.
Mutuwar mutanen ya tsorata al’ummar yankin inda suka nemi mahukuntan kasar da su cece su daga wannan bala’I saboda shaye shayen ya kai ga matan aure da ma dattijan gari.
Shugaban gundumar Malbaza, wanda kuma shine wakilin gwamnati tare da wasu jami’an tsaro da sarkin Dogarawa sun isa garin Gidan Iddar inda suka gana da hakiman garuruwan da bala’in ya shafa.
Shugaban gundumar Malbaza Malam Marafa Tankari y ace za su dauki matakai na ba sani bas abo game da masu sayar da kwayoyin da masu ajiye masu sayarwa a gidajensu tare da wadanda suke kawosu cikin garuruwansu. Malam Marafa Tankari y ace daga yanzu doka ce za ta yi aikinta saboda abun da ya faru abun da doka ta hana ne. Domin gudun musguna ma mutane ya sa ba sa shigowa cikin jama’a su yi aikinsu. Yanzu za su yi aikinsu kuma ba za su yadda wani ya taho ya yi masu katsalandan ba.
Sarkin Dogarawa y ace duk wanda ya saukar da masu sayar da kwayoyi a gidansa idan an kama shi, zai dandana kudarsa.
Shugaban rundunar tsaro na gundumar Malbaza ya yi kira ga hakiman yankin da su tashi tsaye su yaki wannan muguwar dabi’ar. Y ace sun san masu aikata laifin amma suna tsoron kada a zarge su da kai ‘ya’yan wasu gidan yari. Dalili ke nan, yasa suna kallon masu laifin suna kyalesu. Ya ce amma yanzu da suka kira hukuma ta shiga za su sa ido su ga irin hobasan da za su yi.
A saurari rahoton Haruna Mamman Bako domin karin bayani
Facebook Forum