Yanzu dai ta tabbata dukkan shugabannin majalisar dokokin Najeriya da shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara sun koma babbar jam’iyyar adawa ta PDP.
Ba za a gane tasirin yadda za su ci gaba da zama kan mukaman su ba sai majalisar ta dawo zama.
Tuni Sanata Adamu Aliero wanda tun farko ya aza alhaki kan ‘yan sanda da su ka turo gaiyata ga Bukola Saraki, ya ce duk da haka APC za ta ci gaba da zama mai rinjaye.
Da ya ke an shiga lokacin neman zabe, masu fatar zuwa majalisar dokokin tarayyar na baiyana rawar da za su taka in an ba su dama da su ke cewa ba romon baka ne.
Auwal Lalla daga Yobe, wanda ya yanki takardar izinin takarar majalisar wakilai ya na mai cewa zai so zama wakili ne don kawar da yaudarar ‘yan siyasa. Yace ya roki Allah y aba shi damar cika alkawuran da ya yi
Shi kuma Alhaji Sanda Garba Izge daga Borno ta kudu ya ce in ya samu dama zai goyi dorewar mulkin dindindin na Shugaba Muhammad Buhari.
A na sa bangare tsohon dan majalisa a inuwar CPC ta Buhari Barista Ibrahim Bello da ya fice daga APC zuwa PDP, ya na mai cewa canjin da a ke nema bai samu ba. Y ace ba’a san da zaman su ba, ba’a tunanen su saboda haka babu wani dalilin ci gaba da kasancewa cikin APC tunda ba addini ba ne.
Da alamu dai za a yi ta zaman doya da manja ne har karshen wa’adin majalisar da zaben 2019 zai shata sabon fage ga jagorancin majalisun.
A saurari rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya
Facebook Forum