Kungiyar matasan Fulani ta Jonde Jam ta bukaci gwamnatin tarayya da ta sake duba matsalolin makiyayan jahar Filato da suka shafi ilimi da kiwo don magance su.
Shugaban kungyar, Alhaji Saidu Maikano, ya ce, gwamnatin jahar Filato ba ta cika alkawuran da tayi wa makiyayan jahar ba, a lokacin da take neman zabe ba.
A bangare guda kuwa, Abdulkarim Bayero da ke zama tsohon shugaban matasan kungiyar Miyetti Allah ta kasa ya ce, makiyayan jahar Filato sun amfana daga wannan gwamnati.
Sakataren jami’iyyar APC a jahar Filato, Bashir Musa Sati ya ce, gwamnati ta gyara makarantun Fulani makiya.
Shugaban kwamitin sasanta makiyaya da manoma, kuma shugaban CAN na jihohin arewacin Najeriya, Rabaran Yakubu Pam, ya shawarci duk mai wata matsala da ya bi hanyar da ta dace wajen isar da kokensa wa hukumomi.
Ga cikakken rahoton wakiliyar Muryar Amurka, Zainab Babaji.
Facebook Forum