Majalisar Dinkin Duniya ta ce, kusan rabin daukacin adadin kananan yara a nahiyar Afirka ba a yi musu rijista ba a lokacin haihuwarsu, abin da ta ce na shafar damar da suke da ita ta kai wa ga wasu ababan more rayuwa, kamar na kiwon lafiya da kiwon lafiya.
Majalisar ta kuma ce matsalar, ta fi kamari ne a yankunan karkara, inda ake haifar yara a gida, ba tare da iyayensu sun je sun yi musu rijista ba.
An dago wannan batun ne a gefen taron ministocin kasashen Afirka da fannin yin rijistar yara ke karkashin ma’aikatunsu, wanda yake gudana a Zambia.
A cewar wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya a yankin Zambia, Coumbia Mar Gado, rashin yin rijistar na yin mummunan tasiri wajen ginawa yaran rayuwa mai inganci.
Ta kara da cewa, “idan ba ka yi wa yaranka rijista ba, tamkar ba a san da zamansa ba ne, a kasashen Afirka da dama, ba za ka iya saka yaranka a makaranta ba idan ba shi da rijistar haihuwa.”
Facebook Forum