Kungiyar lauyoyi mata ta Najeriya ta sha alwashin bin diddigi don ganin an zartar da hukuncin da ya dace akan wadanda ke da hannu a batun sace wasu yara, aka kuma yi safarar su daga jihar Kano zuwa yankin kudancin kasar domin sayarwa.
A karshen makon jiya ne rundunar ‘yan sandan Kano ta yi holin wasu mutane da aka kama da yara 9 da suka sace a birnin Kano, kuma su ka yi safararsu zuwa birnin Anaca na jihar Anambra.
Yaran su 9 maza da mata na daga cikin jimlar yara fiye da 50 da aka sace a unguwannin Kawo da Hotoro Tishama a lokuta daban daban cikin shekaru uku da suka shude.
Malam Auwalu Ango, uba ga daya daga cikin yaran da aka ceto. Sai Malama Jamila, mahaifiyar yarinya Amira ‘yar shekaru 4, wadda tana cikin yaran da aka ceto, sun ce, da aka fada musu an gano yaran su, sun ji dadi sasai, kuma sun gode wa Allah.
Yanzu haka dai kungiyar mata lauyoyi ta Najeriya da ke rajin kare hakkin mata da kananan yara ta sha alwashin bin diddigin wannan lamari, domin ganin an gurfanar da masu hannu a gaban shari’a. Barrister Amina Umar itace sakatariyar reshen jihar Kano na kungiyar.
To sai dai, iyayen da har yanzu ba’a kai gano ‘ya’yan su da aka sace ba kamar Mallam Shuaibu Ibrahim wanda ke cikin jerin iyaye kusan 50 da aka sacewa yaya kuma har yanzu babu labarin su. Sun ce suna fatan gwamnati ta shigo cikin al’amarin ta taimaka wa jami’an ‘yan sanda domin suma a gano yaransu.
Tuni dai kwamitin dattawan Kano karkashin jagorancin Alhaji Bashir Tofa ta fitar da wata sanarwa mai kunshe da laffuzan jan kunne da jan hankali game da wannan batu.
Ga cikakken rahoton wakilin Muryar Amurka a Kano, Mahmud Ibrahim Kwari.
Facebook Forum