A wani taron gaggawa da shugabannin kungiyar suka gudanar a Kano, sun amince da wannan mataki la’akari da ita hukumar DPR shiyyar Kano ta dauka na kwacewa tare da rarraba albarkatun Man Fetur din ‘ya ‘yan kungiyar kyauta ga masu ababen hawa.
Shugaban Shiyyar Kano na kungiyar Alhaji Bashir Ahmad Dan Mallam, yace “ A matsayin kungiyarmu a matsayinmu na yan kasa masu bin doka da oda, muna bada umarni cewa duk wani memba namu idan ya sami kayannan indai bana gwamnati bane wanda ya kai farashin gwamnati, zai kuma zo ya sayar dashi akan farashin gwamnati to kar ya karya kara daukowa ya dakata saboda bazamuyi ta asara ba.”
Tuni masu kula da al’amura suka fara tsokaci game da wannan batu ganin yadda wannan takaddama ka iya kara jefa al’umma cikin karin tsananin wahala ta albarkatun Man Fetur. Mallam Bashir Mohammad Bashir, mai sharshine kan al’amuran yau da kullum a jihar Kano, yace dole ne gwamnatin tarayya ta kira ‘yan IPMAN da ‘yan DPR ta kuma fayyacewa kowa irin menene aikinsa, domin bukasa da kyautata harkokin kasuwanci.