Hukumar ta bayyana hakan ne a wani rahoton da ta fitar a yau Litinin, yayin da ake bikin ranar yin dubi kan cutar a duk fadin duniya.
Wani shiri da aka tsara domin yaki da cutar a tsakanin shekarun 2016 zuwa 2030, wanda hukumar ta WHO ta amince da shi, ya yi nuni da cewa akalla kasashe goma ake sa ran za su kawar da cutar a duk fadin duniya nan da shekarar 2020.
Sai dai hukumar ta WHO ta yi kiyasin kasashe 21 ake sa ran za su kawar da cutar, wacce sauro ke haddasa, cikin har da wasu kasashen Afrika shida.
Tun daga shekarar 2000, asarar rayukan da ake yi sanadiyar zazzabin cizon saura, ta ragu da kashi 60 cikin dari a duk fadin duniya.
Kasashen da ake sa ran za su kawo karshen cutar a Afrika nan da shekara ta 2020, sun hada da Algeria, Botswana, Cape Verde, Comoros, Afrika ta Kudu da Swaziland.