Kayan tallafin da gwamnatin jihar Neja ta kaiwa 'yan gudun hijiran, sun hada da kayan abinci da baburan hawa da kuma jiragen ruwan kwale-kwale.
Bayan da aka mika masu kayan tallafin gwamnan jihar Alhaji Abubakar Sani Bello, yace sun dauki matakin ne saboda mutanen suna cikin wani hali mai tada hankali. Idan aka ce mutum ya bar gidansa da garinsu alatilas, wajibi ne gwamnati ta taimaka masa. Gwamnan ya yi fata nan ba da dadewa ba za'a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali domin kowa ya koma gidanshi.
Dangane da tsaro, gwamnan yace 'yansanda da mutanen da suke zaune cikinsu suna sa masu ido domin kada a samu bata gari.
'Yan gudun hijiran sun nuna godiya kan tallafin da gwamnatin jihar ta basu to amma sun ce suna fama da rashin magani a sansanonin da suke kasancewa akwai wasu da dama a cikinsu dake fama da rashin lafiya.
Inji ta bakin wani dan gudun hijira, yace akwai mutane dake fama da cuta. Wasu idan an kaisu asibiti sai a ce basu da jini sosai a jikinsu. Kafin a yi karo karon kudi wasu sun rasa rayukansu.
Shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Neja Alhaji Ibrahim Inga yace suna yin wani abu akan batun magani. Yace ya samu kwamishanan kiwon lafiya na jihar wanda nan take ya soma shirya yadda za'a kai masu magunguna.
Ga karin bayani.