Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar BBOG Dake Fafutikar Neman A Sako 'Yan Matan Da Aka Sace Ta Canza Salo


 Gangamin BBOG a Abuja akan 'yan matan da aka kara sacewa
Gangamin BBOG a Abuja akan 'yan matan da aka kara sacewa

A gangamin da ta yi bakin kofar shiga fadar shugaban kasa, kungiyar BBOG ta yi juyayi akan yadda aka kara sace wasu 'yan matan har 110 ta kuma mika tambayoyi 14 dake bukatar amsoshi daga gwamnati cikin mako daya ko kuma ta ruga zuwa kotu shigar da kara

A taron manema labarai da kungiyar BBOG ta kira a daidai kofar shiga fadar shugaban Najeriya ta Aso Rock, tsohuwar ministar ilimi kuma jagorar kungiyar Obi Ezekwesili ta ce kungiyar zata canza salonta.

Manufar canza salon domin ta kalubalanci gwamnati ne wajjen ganin an kwato sauran 'yan matan cikin sauri.

Inji Obi Ezekwesili "muna cikin fushi da juyayi yadda gwamnati ta yi sakaci aka sake maimaita abun da ya faru a Chibok shekaru hudu da suka gabata. Yanzu haka an sake sace 'yan mata 110 a jihar Yobe dake arewa maso gabashin Najeriya"

A lokacin da take ci gaba da bayani, Obi Ezekwesili ta yiwasu tambayoyi guda goma sha hudu dake bukatar amsoshi daga bangaren gwamnati.

Edith Yasin jigo a kungiyar ta yi karin haske akan batun. Ta ce duk tambayoyin da aka yi gwamnati ta yiwa Allah ta bada amsoshinsu. Idan kuma ba'a bada amsoshin ba ke nan babu abun da ake yi akan 'yan matan da aka sace.

Shi ma babban lauyan kasa Femi Falana ya yi karin haske akan hurumin da kundun tsarin mulki ya ba gwamnati.Hakkin gwamnati ne ta kare lafiya da dukiyoyin duk 'yan Najeriya.

Kungiyar ta ce nan da mako daya idan bata samu amsoshin tambayoyin da ta mika ba, zata shigar da kara a kotu.

Medina Dauda nada karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:26 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG