Wani jirgin sama mai saukar ungulu mallakar kamfanin Bristol Helicopters ya rikito a tekun Atlantica, dake jihar Lagos.
Rahotanni dake fitowa daga yankin dai na nuna cewa fasinjoji 11, da kuma matuka 2, ne ke cikin wannan jirgi, a lokacin da ya fado .
Kakakin hukumar agajin gaggawa mai kula da yammacin Najeriya Mr. Ibrahim Farinloye, yace a lokacin da da muka sami rahoton faduwar wannan jirgin tare da taimakon rundunar Sojojin ruwan Najeriya, an ceto fasinjoji 11, da matuka jirgin saman 2, kuma yanzu haka suna samun kulawa a wani asibiti a birnin Lagos.
Yanzu haka bangaren dake kula da hadarin jiragen sama na Najeriya zai gudanar da binciken faduwar wannan jirgi.
Wannan ne dai9 karon na 2, a kasa da watani 2, da jirgin sama mai saukar Ungulu malakar kamfanin Bristol, ya fado akasarin jiragen na Bristol, yana jigilar ma’aikata ne dake aikin hako mai a Teku.
HUkumar kula da filayen jiragen saman na Najeriya, ta tabbatar da faduwa wannan jirgi, kamar yadda suka sheda wa wakilin muryar Amurka, sun ce hukumar dake gudanar da bincike da kuma kula da lafiyar jiragen sama ta Najeriya, sune zasu yi bayani game da faduwar wannan jirgi, har lokacin hada wannan rahoto dai manyan jami’an hukumar na gudanar da bincike game da afkuwar wannan hadari.