Kotun dai ta yanke hukunci kan barin mata musulmai su rika sanya hijabi zuwa makaranta, bayan hukuncin da alkalan uku suka yanke a karkashin jagorancin alkali M.L Garba.
Sun kuma ce gwamnatin za ta iya daukaka kara kan karan da suka shigar na neman a hana dalibai zuwa aji da hijabi.
Alkalan dai sun bayyana cewa ‘yanci ne na bil adama dake karkashin tsarin mulkin Najeriya, wanda ya baiwa ‘yan kasar ‘yancin gudanar da addinin da suka ke so, don haka hana ‘dalibai zuwa aji da hijabi na nufin tamkar an tauye musu hakkinsu ne.
Lauyan gwamnati ya bayyana cewa gwamnatin jihar za ta daukaka kara zuwa kotun ‘kolin tarayyar Najeriya.
Sai dai lauyan masu gabatar da kara ya bayyana cewa ba su da wata gardama game da bukatar da gwamnatin jihar ta gabatar na cewa za ta daukaka kara game da wannan hukunci.
Yanzu haka dai wasu mazauna jihar Legas na nuna gamsuwa da jin dadinsu ga wannan hukunci da kotun ta yanke, don baiwa duk ‘yan ‘kasa damar yin addinsu ba tare da nuna tsangwama ba.
Domin karin bayani saurari rahotan Babangida Jibrin.