A hukuncin da mai shari'a Muhammad Idris Kutigi ya gabatar bisa karar da wata kungiya ta kai gabansa ya umurni gwamnatin tarayyar Najeriya da ta bayyanawa 'yan kasar yadda ta kashe kudaden sata da ta kwato.
Kungiyar mai suna SERAF tana bin digdigin yadda ake gudanar da tattalin arziki da kuma rayuwar al'umma a Najeriya ita ta shigar da kara a gaban kotun inda take neman gwamnati ta bayyana yawan kudade da kadarorin da ta kwace daga wadanda suka wawuresu a shekarun baya zuwa yanzu. Alkalin yace bukatar kungiyar ta yi daidai da dokar samun bayanai ta shekarar 2011.
A martanin da suka mayar akan hukuncin mataimakin daraktan SERAF Mr. Olukayode yace hukuncin ya tabbatar da zargin da su keyi wa gwamnatocin da suka gabata na gazawa tunda kan gwamnatin Chief Obasanjo zuwa ta Goodluck Jonathan akan baiwa al'ummar kasar bayanan yadda suka kashe kudaden gwamnati kamar yadda kundun tsarin mulkin kasa ya tanada.
Masu fashin baki kan lamuran siyasa da shari'a na ganin hukuncin wani dama ne da gwamnati mai ci yanzu dake yaki da cin hanci da rashawa ta samu na jan damara a kokarin da ta keyi a yaki da cin hanci da rashawa.
Dr Danlami Alhasan Abubakar na sashen koyan aikin jarida a Jami'ar Bayero ya bayyana mahimmancin hukuncin. Hukuncin ya kawar da dodorido da gwamnati ta ke yiwa 'yan kasa. Kowa nada ikon ya nemi bayani akan komi gwamnati ta keyi musamman nawa ta tara nawa ta kashe da kuma yadda ta kashesu.
Yanzu dai an sa ido a gani ko gwamnati Muhammad Buhari zata daukaka kara ko kuma zati bi umurnin kotun.
Ga karin bayani.