A yan kwanakin nan dai sai da farashin dalar Amurka ta kai har Naira 400 a kasuwar bayan fage, yayin da a hukumance take Naira 199. Alhaji Mohammadu Mustapha Muntube, tsohon babban manajan daraktan Bankin Jaiz wanda yake masanin tattalin arziki. Na ganin kafin ayi gyara dole ne a matsar da darajar Naira ta kai kamar 250 a hukumance, haka kuma dole ne babban banki ya dauki matakan da suka kamata.
Shi kuma wani kwararre kan tattalin arziki a Najeriya, Abubakar Ali, na da ra’ayin da ya banbanta da na Alhaji Mohammdu, inda yace idan har aka mayar da Dala ta koma Naira 250 a hukumance to tabbas kasuwar bayan fage zata koma 500, a cewarsa haka al’adar kasar take.
A karin hasken da Muhammadu Mustapha Bintube yayi, yace yakamata babban bankin tarayya ya san yadda zai yi ya dauki matakan da sauran kasashen duniya ke dauka na yadda kudadensu basa canzawa a kasuwa.
Domin karin bayani.