Lauya mai zaman kansa dake zaune a birnin Abuja, Umar Zaga, ya kare Lauyoyi da cewa, ba wai suna kare masu laifi bane, suna dogaro da damar da ke karkashin doka. Inda yace sautari a Najeriya, ana gurfanar da mutum kan wani laifi amma sai a kasa kawo hujja da za a ci gaba da Shari’a, daga baya kuma sai a zargi Alkali ko lauyoyi da laifi. Zaga, yace dole ne a sake duban wannan tsari domin samun nasara ga wannan yakin da ake.
Shi kuma shugaban Rundunar Adalci, Abdulkarim Dayyabu, na ganin sai shugaba Buhari ya kara matsa kaimi wajen bincikar sauran sassan gwamnati, ta hakane kawai Najeriya za ta inganta.
A nasa bangaren dan siyasa Adamu Bunu Yadi, na ganin yan Najeriya na nuna gajen hakuri kan alkawuran da gwamnatin Buhari ta dauka. Inda yake ganin Buhari zai tarawa kasar kudi, wanda shugabannin gaba ba zasu sami wata matsala ba.
Jam’iyyar APC mai mulki dai ta kare tafiye tafiyen shugaba Buhari, da cewa nan bada dadewa ba za a ga tasiri ga ingantar tattalin arzikin kasar da yake a komade.
Domin karin bayani.