Bisa ga alamu, musamman idan aka yi la'akari da kalamun mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin shari'a Okoi Obono-Obla, nan ba da dadewa ba bangarorin hukumar shari'a da na zartaswa zasu shiga kafar wando daya.
'Yan fafutikar yaki da cin hanci da rashawa su ma zasu ja da bangaren hukumar shari'a wadda ta yanke shawarar maida alkalan da aka samesu da makudan kudade ana kuma zarginsu da cin hanci da rashawa bakin aikinsu.
Can baya dai cikin alkalan takwas an gurfanar da uku cikinsu gaban kotuna.
Mai baiwa shugaban kasa shawara akan harkokin shari'a Mr. Okoi Obono-Obla ya bayyana rashin jin dadin gwamnatin tarayya akan matakin da hukumar shari'a ta dauka na maida alkalan bakin aikinsu. Yana mai cewa tamkar kafar angulu ne a ke yiwa yaki da cin hanci da rashawa. Yace babu wani dalilin maidasu bakin aiki a daidai lokacin da hukumar ta san ana yunkurin gurfanar dasu gaban kuliya.
Amma a cikin sanarwar da hukumar shari'ar ta fitar tace biyar daga cikin alkalan ne aka maida bakin aikinsu saboda ministan shari'a da ya bukaci a dakatar dasu bai gurfanar dasu a gaban kuliya ba cikin watanni takwas..Sanarwar tace babu dalilin da za'a hanasu aikinsu saboda ba'a gurfanar dasu ba bisa zargin da ake yi masu ba.
Dr Ahmed Sale daraktan daya daga cikin kungiyoyin dake fafutikan yaki da cin hanci da rashawa yace matakin da hukumar shari'ar ta dauka babbar matsala ce ga yaki da cin hanci da rashawa. Abun da hukumar tayi ta nunawa 'yan Najeriya cewa tun farko hukumar shari'a bata goyon bayan shugaban kasa kan yaki da cin hanci da rashawa. Yana cewa dalili ke nan da suke rajin an kafa kotu ta musamman da zata kula da batun cin hanci da rashawa.
Ga rahoton Umar Faruk Musa da karin bayani.
Facebook Forum