Tun can farko ministan yada labarun Najeriya Alhaji Lai Muhammad yace shugaban yana hannun kwararru dake kula da lafiyarsa a birnin London can kasar Birtaniya.
Labarin samun saukin shugaban a wannan karon ya dauki wani salo daban inda wasu kafofin labaru suke yada labarin da bashi da tushe. Wasu sun ce wai guba ne ya ci amma ya sallake rijiya da baya. Wasu ma sun yi anfani da hotonsa inda yake gaisawa da tsohn shugaban Ingila David Cameron. Dukansu labarai ne da basu da tushe.
Ahmadu Tsaida wani tela dake arewa maso gabas yana fatan shugaban ya dawo lafiya ya cigaba da ayyukansa amma ya gargadeshi ya dinga la'akari da masoyansa na gaskiya. Ya karbi shawarwari, ya kuma aiwatar da gyaran da ya dace.
A yayinda wasu ke yabawa mataimakin shugaban saboda sanin aiki shi ko gwamnan jihar Ekiti kira yayi ga shugaban yayi murabus. Yace shekaru biyun da Buhari yayi kan mulki wani sabanin samun sa'a ne ga kasar.
Shi ko Yau Ciroman Bankan Daura na hannun daman shugaba Buhari yace yau babu maganar Boko Haram saboda haka akan maganar tsaro PDP bata da bakin magana. Yace yanzu hankalin mutane ya kwanta, kowa na barci yadda yakamata. Ana tafiya a hanya babu fargaba.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.
Facebook Forum