Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Koriya ta Arewa Ta Saki Hotunan Makami Mai Linzami Samfurin Ballistic Da Tayi Nasarar Kerawa


Sabon Makami Mai Linzami da Koriya ta Arewa ta harba Mai Nisan Zangon Nahiya zuwa Nahiya
Sabon Makami Mai Linzami da Koriya ta Arewa ta harba Mai Nisan Zangon Nahiya zuwa Nahiya

Amurka tayi kira da a dakatar da duk wata mu'amala da akeyi da Koriya ta Arewa.

Koriya Ta Arewa ta saki wani Bidiyo da ya nuna shugaban kasar Kim Jong Un yayin da yake kallon harba makami mai linzami mai ratsa nahiyoyi da ake kira ICBM a takaice da turanci.

Rahotanni sun ce an harba makamin ne jiya da safe daga wani wuri dake arewacin babban birnin kasar Pyongynag. Sabon makamain ya yi tafiyar kilomita dubu hudu da dari biyar, wanda ya nunka har sau goma inda tashar binciken dake sararrin samaniya ta ke, kuma ya yi tafiyar kilomita dubu kafin ya fada cikin tekun Japan ta gabashin makurdin koriya.

Duk da shakkun da masu fashin baki suka yi kan kwari da tasirin makamin, jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Niki Haley, tayi gargadi jiya Laraba cewa "gwajin makamin mai linzami na baya bayan nan, ya kara tura duniya kusa da fadawa yaki, ba nesanta ta daga fitinarba." Haka nan tayi kira ga kasashe dake Majalisar Dinkin Duniya su yanke huldar jakadanci da Koriya ta Arewa, ta ko wanne mataki da hulda.

Jakadiya Haley, ta ce shugaba Trump ya gayawa takwaransa na China Xi Jinping ta wayar tarho a jiya Laraba cewa lokaci yayi da China, zata dakatar da duk jigila ko sayarwa Koriya ta Arewa mai.

Da yake magana kan gwajin makamin a jiya Laraba ta shafinsa na Tweeter, shugaban Amurka Donald Trump, yayi alkwarin kakabawa gwamnatin ta Pyongyang wacce ta zama saniyarware takunkumi kai tsaye ba tareda gudumawar wani ko wata kasa ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG