A wajen wani taron sujadar da dubban ‘yan Myanmar suka hallarta a birnin Yongon, birni mafi girma a Myanmar, yau Laraba Fafaroma Francis yayi magana akan bukatar yin gafara da kuma kaucewa yin ramuwar gayya.
Sai dai karo na biyu ke nan kai tsaye bai ambaci batun kisa da kuntatawar da aka yiwa musulmin Rohingya ba a ziyarar da yake yi ta kwanaki 4 a kasar, bayan da yayi jawabi akan mutunta addinin wasu a wata ganawa da yayi da jami’an diplomasiyya jiya Talata.
Fafaroma, wanda ke yawan jan hankali akan a taimakawa ‘yan gudun hijira, ya ba mutane dayawa daga kasashen yammacin duniya mamaki, wadanda suka yi hasashen zai yi magana akan rikicin Rohingya a bainar jama’a.
‘Yan Rohingya fiye da 620,000, tsirarun musulmin da aka dade ana kuntatawa ne suka tsere daga kasar zuwa Bangladesh tun daga watan Agusta bayan wani farmaki da sojojin kasar suka kai masu.
Facebook Forum