Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Baikon Yariman Birtaniya Harry Da Meghan Markle


Britain's Prince Harry poses with Meghan Markle in the Sunken Garden of Kensington Palace, London, Britain, Nov. 27, 2017.
Britain's Prince Harry poses with Meghan Markle in the Sunken Garden of Kensington Palace, London, Britain, Nov. 27, 2017.

A hukunce an yi baikon Yarima Harry na Birtaniya da ‘yar wasan fina finai Ba Amurkiya Meghan Markle.

Mahaifin Harry, Yarima Charles ne ya sanar da haka a wata sanarwa jiya Litinin.

“Mai martaba Yariman Wales yana farin cikin sanar da baikon Harry da Ms Meghan Markel”

Sanarwar tace za a yi auren ne da kakar shekara ta dubu biyu da goma sha takwas, za a kuma bada Karin haske a kan bukin auren nan gaba.

Iyayen Markel suma sun fitar da sanarwa cewa, “muna matukar taya Meghan da Harry murna.

Markel tana da ruwa biyu. Mahaifina bature ne mahaifiyarta kuma bakar fata.

Markel tace taji takaicin yadda kafofin yada labarai suka rika bibiyar jinsinta, sai dai ta kara da cewa, ita da Harry, basu taba maida hankali a kan wannan ba, muna maida hankali kawai akan yadda rayuwarmu zata kasance tare.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG