Ranar Lahadi 15 ga watan Nuwamba Shugaban yankin Tigray da ke arewacin kasar Habasha ya tabbatar da cewa dakarunsa sun harba makamai masu linzame a Asmara babban birnin kasar Eretria, ya kuma yi barazanar kara kai wasu hare-haren, yana mai cewa zasu auna duk wani abu da ya shafi soja kuma zasu kai hari.
Shugaban yankin Tigray Debrestsion Gebremichael bai fadi yawan makamai masu linzamen da aka harba Asmara a jiya Asabar ba, amma ya ce shi kadai ne birnin Eretria da aka kai wa farmaki.
Kalamansa sun tabbatar da ruruwar rikicin da ke faruwa tsakanin kasashen makwafta biyu na Afrika yayin da fadan da ake yi a Tigray ya riga ya bazu zuwa tsallaken iyaka.
An harba rokoki 3 a Asmara a jiya Asabar, a cewar wasu majiyoyin diflomasiyya sa’o’i bayan da shugabannin yankin Tigray na Habasha suka yi gargadin ta yiwu a kai farmaki.
Facebook Forum