Hukumar zaben Kenya ta ce, ya zuwa daren jiya Laraba, an kidaya kashi 96 cikin 100 na adadin rumfunan zaben kasar, inda shugaba Uhuru Kenyatta yake da kashi 54 cikin 100 yayin da shugaban ‘yan adawa Raila Odinga ya samu kashi 44.
Jami’ai a hukumar zaben kasar na da tsawon mako guda su bayyana sakamakon zabe kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.
Sai dai Odinga yana zargin cewa an yi abinda ya kwatanta a matsayin “gagarumin kutse” a na’urorin kwamfutar hukumar zaben, lamarin da ya sa ya ce zaben na cike da kurakurai.
Amma shugaban hukumar zaben, Ezra Chiloba,ya ce, ya zuwa yanzu ba su ga wata alama da ta nuna cewa an yi kutse a nu’ororinsu ba.
Shugaba Kenayatta da Odinga, sun jima suna hamayyar siyasa a tsakaninsu, inda a baya suka taba karawa a shekarar 2007 da 2013.
Zaben 2007 ya haifar da tarzomar da ta kai ga hasarar rayuka da dama.
Facebook Forum