Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Mayarwa Shugaban Nijar Martani Kan Kiran Al'ummomin Kasar Su Rage Haihuwa


Shugaban Nijar Issoufou Mahammadou
Shugaban Nijar Issoufou Mahammadou

Wasu 'yan Nijar da malaman addinin Musulunci sun mayarwa shugaban kasar Nijar Issoufou Mahammadou martani kan kiran da yayi na cewa 'yan kasarsa su rage haihuwa

Yawan al'ummar Nijar zai nika sau biyu zuwa miliyan 35 nan da shekaru 18.

Karin na nufin nan da shekarar 2035 yawan al'ummar Nijar ka iya haurawa miliyan 40, kuma watakila ya dangana kusan miliyan 75 a shekarar 2050,

Inji shugaban kasar Nijar Issoufou Mhammadou idan so samu ne tun yanzu ya kamata a fara hangen ta yadda za'a bullowa wannan kalubalen dake jan hankulan 'yan kasar game da yawan mutane.

Amma da alama wasu 'yan kasar basu gamsu da kalamun na shugaban kasa ba. Wasu na tambaya mata nawa shugaban kaye dasu kuma 'ya'yansa nawa. Suna ganin talaka ne yake son ya takura.

Al-Kasumu Abdulrahaman na ganin idan saboda karancin abun kula da karin mutane ne ya sa shugaban ya kira a rage haihuwa, shi ko yana ganin bunkasa tattalin arziki ne ya kamata a maida hankali a kai domin warware matsalolin jama'a. Bunkasa tattalin arziki ya fi a gayawa mutane su rage haihuwa.

Malaman addinin Musulunci ma sun shiga tunatar da al'umma abun da addinin ya tanada game da haihuwa. Uztas Aja na kungiyar Malaman Islama yace musulunci bai yadda a saki iyali barkatai ba amma kuma Allah yace kada musulmi ya ji tsoron haihuwa saboda tsoron yunwa. Yace tsarin turawa ba na musulmi ba ne.

To saidai malamin yace kafin mutum yayi iyali ya san abun da ya tanada masu dangane da iliminsu, da tufafinsu da cimakarsu da kiyaye lafiyarsu.

Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG