A Rwanda, hukumar zaben kasar tace shugaba Paul Kagame ya sami nasarar wa'adi na uku bayan da ya lashe zaben kasar da gagarumar rinjaye.
Hukumar ta ce kwariya-kwariyar sakamakon zaben da aka gudanar jiya jumma'a, ya nuna cewa shugaban ya sami kashi 98 cikin dari. A wani gangamin yakin neman zabe cikin watan Yuli, shugaba Kagame ya gayawa magoya bayansa cewa "ranar zabe rana ce da za'a tabbatar da abunda aka riga aka sani."
A jawabinsa shugaba Kagame yace "wannan wasu shekaru bakwai nedomin domin tunkarar matsaloli da suka dami 'yan Rwanda, kuma tabbatar da cewa mun kasance cikakkun 'yan Rwanda wadanda suke samun ci gaban tattalin arziki.
Abokanan hamayyarsa sune Frank Habineza na jam'iyyar Green party, da kuma dan Indipenda Philippe Mpayimana.
Shakaru 17 kenan Kagame yake mulkin kasar. Wata kuri'ar raba gardama kan kwaskwarima ga tsarin mulkin kasar da aka yi a 2015 wanda kashi 98 cikin dari na jama'a suka amince da shi, zai baiwa shugaba Kagame damar ci gaba da mulki kasar har zuwa shekara ta 2034.
Ana aza nasarar daidaita kasar bayan kisan kare dangi da aka yi a 1994 kan shugabancin Kagame.
Facebook Forum