Kwararre kuma mai bada shawara akan bunkasa aiki da iskar gas na ofishin mataimakin shugaban Najeriya, Dayo Adesina yace, baya ga mutane kimanin kashi biyar da ke da damar amfani da iskar gas wajen girki, akwai kaso sittin daga cikin dari na masu amfani da itace, kashi talatin kuma da kalanzir suke amfani, kashi biyar kuma suna amfani ne da bakin gawayi wajen girki.
Babbar matsalar da aka gano a binciken ita ce, kashi casi’in cikin dari na tukwanen iskar gas da ake amfani dasu wajen girki a Najeriya, sun gama aiki, domin ana bukatar duba lafiyar tukunyar gas ko sauyata duk bayan shekaru goma sha biyar.
Mr. Adesina yace kashi talatin cikin dari na tukwanen sun kai shekaru talatin da gama aiki, don haka sun zama barazana ga rayuwar mutane don akwai yiwuwar tashin gobara ta tukwanen. Bayan gobara kuma, masana na duba tasirin wannan lamari ta hanyar zabar hanyoyin da basa karewa wajen samun makamashi da kare lafiyar muhalli.
Farfesa Sani Sambo, tsohon babban daraktan hukumar Makamashi ta Najeriya, yace makamashin da baya karewa shine wanda a kowanne lokaci akwai shi, amma akwai makamashin da ke karewa, kamar man fetur da iskar gas da kwal da kuma sinadarin Yuraniyum. Ma’ana idan ana amfani da su yau da kullum, za a wayi gari wata rana babu su.
Ya ci gaba da cewa makamashin da ba ya karewa shine na iska, hasken rana da tsirrai da wanda ake samu daga ruwa. Shi kuma Malam Imran Adamu ya bayyana cewa, amfani da gas wani abu ne mai sauki ga rayuwar al’umma idan aka yi la’akari da cewa gas ya fi kananzir sauki, don kudin da zaka sayi gas da su a sati, za su iya saya maka iskar gas din da zai kai wata daya ko biyu.
Bayan hak, gas bashi da matsala irin ta kalanzir ko gawayi da ake amfani da su, saboda ba ya bata lokaci wajen girki kuma baya sa bakin tukunya a cewar malam Imran. Sai dai, Imran yace akwai hadari tattare da amfani da gas musamman ga wadanda ba su san yadda za su yi amfani da shi ba.
Imran Adamu ya karkare da cewa, ya kamata a sa wa kamfanonin da ke sana'ar cika tukwanen da iskar gas ido, domin su bi ka’idodin da suka dace wajen cika tukwannen iskar gas da ake amfani da su wajen girki a Najeriya.
Ga karin bayani cikin sauti a rahoton Wakilinmu.
Facebook Forum