Kungiyar kwadago ta kamfanoni masu zaman kansu TUC ta nuna matukar damuwa ga yadda 'yan Afurka Ta Kudu su ka far wa 'yan Najeriya da cin zarafi har ma da kisa, duk da yadda Najeriya ta taimaki kasar ta samu 'yanci daga wariyar launin fata.
Jami'in kungiyar, Nuhu Toro, ya yi karin bayani bayan sanarwa da kungiyar ta rabawa manema labaru.
Toro ya ce akwai lokacin da ta kai ga ma'aikatan Najeriya su ka tara gudunmawa su ka aikawa kungiyar gwagwarmayar bakaken fata ta ANC karkashin marigayi Nelson Mandela.
Sai dai kungiyar TUC ta bukaci shugaban Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, ya dau matakan hana bata gari kai hari kan 'yan Najeriya da al'ummar wasu kasashen da ke zaune a kasar.
Duk da haka, TUC ta ce ba daidai ba ne huce haushi da wasu matasan Najeriya su ka yi kan kamfanin sadarwa na MTN da kasuwar Shoprite duk mallakar 'yan Afurka Ta Kudu a manyan biranen Najeriya.
Saurari cikakken rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya daga Abuja:
Facebook Forum