Gwamantin Sin ta bayyana manyan matakan da zata dauka, wanda ta yi amannar zasu ci gaba da bunkasa tattalin arzikinta a matsayin kasa ta 2 a duniya mafi karfin tattalin arziki.
Wanda suke son tattalin arzikin nasu ya haura da akalla kaso 6 da digo 5 a shekarar nan ta 2015 da muke ciki, duk kuwa da tafiyar hawainiyar tattalin arzikin da ake samu a duniya da zaftare ayyukan da ake gani a masana’antu.
Firimiyan birnin Sin Li Keqiang ne ya bayyana haka, inda ya kara da cewa, sun maida hankali sosai ga kayayyakin da ake sarrafawa a cikin gida. Shima wani memba a kwamitin tuntuba na siyasar China yayi karin haske.
Da cewa an yi wannan kiyasin ne don a rage tsammanin da ya wuce kima. A bara dai, Sin ta cimma nasarar tattalin arziki da kaso 6 da digo 9, wanda haka ya dan yi kasa da kaso 7 bisa yadda suka so cimma.