Masu lura da al’amura dai sun ce har yanzu yarjejeniyar nan ta Minsk bata mutu ba. A shekaran jiya Alhamis ne Ministocin harkokin wajen kasashen Faransa, Jamus, Rasha da Ukraine suka hadu a birnin Paris bisa tsarin nan da su kan kira da Normandy Format.
Iinda suke yunkurin sake dawo da zaman tattaunawar sulhun. Ba a dai cimma tsarin yarjejeniyar ta Minsk ba da aka kulla a watan Fabrairun shekarar 2015, wacce wa’adinta ya cika a karshen shekarar da ta gabatan.
Wani mai tsokaci Jeff Rathke Inda yace, dole sai bangarorin gaba daya na ‘yan awaren da Mascow ke marawa baya da kuma na Kyiv sun yi nasu kokarin in ha rana son cimma tsagaita wutar a tsakaninsu, sannan kuma su yi zaben raba gardama a tsakaninsu.